Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bisa himmar karamin ofishin jakadancin Iran a Dakar, an tarjama fim din wilayat Eshq a cikin harsunan kasar Senegal a daidai lokacin tunawa da zagayowar haihuwar Imam Ali bin Musa Redha (AS) wanda aka tarjama acikin Harsunan Faransanci da Wolf.
Hassan Chao wanda dalibin digiri na uku ne a harshen farisanci a jami’ar Modarres shi ne yake gudanar da aikin tarjamar, wanda ya samu gudunmawa wajen samar da kayar aikin tarjamar daga jami’ar Antadiuop da ke birnin na Dakar tare da taimakon Aisha Jah babbar jami’a a bangaren shirya fima-finan kasa.