IQNA

Martanin Kungiyar Kasashen Larabawa Kan Amincewa Da Kafa Kasar Yahudawa

20:37 - July 21, 2018
Lambar Labari: 3482840
Bangaren kasa da kasa, majalisar dokokin HKI wacce ake kira Knesset ta amince da wata doka wacce ta tabbatar da wariya tsakanin mazauna haramtacciyar kasar, inda ta amince da yahudawa kadai a matsayin yan kasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, bayan amincewa da wannan dokar ta wariya kungiyar kasashen larabawa ta yi allahwadai da dokar ta kuma bukaci kasashen duniya su tashi don sauke wajibin da ya hau kansu na hana dokar wariya da nuna bambanci wacce majalisar Knesset ta amince da ita a jiya Alhamis.

Dokar dai ta yi watsi da larabawa wadanda yawansu ya kai kimani kashi 20 % na yawan mutanen da suke zaune a yankunan da HKI ta ke  mamaye da su. Dokar ta tabbatar da harshen hibru a matsayin harshen da gwamnati da makarantu ta amince da yin watsi da harshen larabci, da kuma fifita yahudawa a kan duk wanda ba bayahude ba a kasar. 

Wannan dokar dai ta HKI tamkar irin ta Afrika ta kudu kafin faduwar tsarin wariya a kasar.

Kasashen larabawa sun kasa tabuka komai a lokacin da aka fara wannan batu, tun daga lokacin ake shirin mayar da ofishin jakadancin Amurka  abirni mai alfarama.

Yayin da kuma wasu  sarakunan larabawan masu munafuntar sauran larabawa da suke hada baki da Isra’ila domin tabbatar da wannan manufa.

3731649

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha