IQNA

Jerin Gwanon Majami’oin Zimbabwe Domin Sulhu

13:19 - July 23, 2018
Lambar Labari: 3482842
Bangaren kas da kasa, majami’oin mabiya addinin kirista  akasar Zimbabwe za su gudanar da jerin gwanon neman a yi zabe cikin cikin sulhu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, majami’oin mabiya addinin kirista  akasar Zimbabwe za su gudanar da jerin gwanon lumana a birnin Harare domin  neman a yi zaben 2018 cikin cikin sulhu da kwanciyar hankali.

Manyan majami’oin birnin Harare fadar mulkin kasar ta Zimbabwe ne suka shirya wannan gangami da jeri gwano, da nufin ganin sun ja hankulan jama’ar kasar kan wajecin kiyaye sulhu da zaman lafiya  akasar a lokacin zabe.

Babban malamin addinin kirista na kasar shi ne ya kira jerin gwanon, inda ya ce suna goyon duk wani mataki da zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da fahimtar juna tsakanin al’ummar kasar.

A cikin wannan shekara dai za a gudanr da zaben shugaban kasa na farko baya kawar da gwamnatin Mugabe da ta gabata a kasar ta Zimbabwe.

3732532

 

 

 

 

 

captcha