IQNA

Kwamitin Tsaron UN Ya Gudanar Da Zama Kan Harin Saudiyya A Yemen

23:44 - August 11, 2018
Lambar Labari: 3482884
Bangaren kasa da kasa, A zaman da kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya ya bukaci da agudanar da binciken gaggawa kan harin Saudiyyah a gundumar Sa’ada da ke Yaman.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, A lokacin da mambobin kwamitin tsaron na din-din-din suka gudanar da zama a jiya, dukakninsu sun amince a kan cewa dole ne a gudanar da bincike kan harin na Saudiyyah da ta kaddamar a garin Sa’adah, wanda ya yisanadiyyar mutuwar fararen hula hamsin da dayatare da jikkatar wasu sabainh da bakawai.

A yayin zaman kwamitin tsaron na jiya, jakadan kasar Birtaniya a majalisar dinkin duniya Karen Pierce ya bayyana harin na Saudiyya da cewa hari ne maras kan gado, wanda ya zama wajibi a yi bincike a kansa.

Kasashen duniya da kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, suna ci gaba da yin Allawadai da harin wanda jiragen yakin Saudiyya suka kaddamar kan wata motar bas da ke dauke da yara ‘yan makaranta a Sa’ada da ke kasar tabYaman, inda fararen hula 51suka rasu, talatin daga cikinsu kananan yara ne ‘yan kasa da shekaru sha biyar.

3737289

 

 

 

 

captcha