Kamfanin dillancin labaran ya habarta cewa, ofishin babban limamin birnin Nairobi na kasar Kenya ya fitar da sanawa kan cewa a ranar talata mai zuwa za a gudanar da sallar idin babbar salla a kasar Kenya baki daya.
Ofishin limamin ya dauki wannan mataki ne domin bin kasar Saudiyya wadda za ta yi salla a ranar Talata, ba wai domin lissafin su ya cika ba.
Haka nan kuma limamin ya kirayi dukkanin muuslmi a kasar ta Kenya baki daya da su fito domin yin sallar idi a koina akasar tare da yanka ragunan layya.