IQNA

Jagora: Manufar Takunkumin Da Bakar Farfagandar Makiya A Kan Iran, Ita Ce Kashe Gwiwar Al'umma

23:40 - September 06, 2018
Lambar Labari: 3482958
Jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewar makiyan al'ummar Iran sun kakabawa Iran takunkumi da kuma ci gaba da yada bakar farfaganda a kanta ne saboda kashe gwiwan al'ummar kasar da kuma sanya musu yanke kauna cikin zukatansu.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a yau din nan da shugaba da 'yan majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran inda ya ce a halin yanzu gwamnatin Musulunci tana fuskantar gagarumin yaki ne a fagen tattalin arziki da kuma kafafen watsa labarai da farfaganda, wanda babbar manufar hakan ita ce kashe gwiwan al'ummar Iran.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da cewa farfagandar da makiya suke yadawa kan Iran ba wani sabon abu ba ne face dai a wannan karon ya dau wani sabon salo ne, Ayatullah Khamenei ya ce: Bisa ga bayanan sirrin da muke da shi, wannan cibiyoyin leken asirin Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila da na wasu kasashen da suke makwabtaka da Iran su ne suke jagorantar wannan farfagandar sannan kuma suna ta kokari wajen ganin sun lalata yanayi a kasar Iran.

Don haka sai Jagoran ya kirayi jami'an bangarori daban-daban na gwamnatin Iran din da su hada kai waje guda tare da samun goyon bayan al'umma wajen fada da wannan makirci na makiyan.

Sai dai Jagoran ya ce duk da irin wannan bakar aniya ta makiya din amma duk da haka al'ummar Iran suna ci gaba da samun ci gaba a bangarori daban-daban na rayuwar duniya da ta lahira.

3744510

 

captcha