Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Alwatan News cewa, a jiya ne wata tawagar manyan jagororin mabiya addinin kirista a Masar sun bayar da kyautar kur'ani ga gwamnan lardin Minya na kasar ta Masar Qasem Hussain Qasem.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wadannan kiristoci sun kai ziyara a babban ginin jahar inda a nan ofishin gwamnan na Minya yake, inda suka gana da shi.
Ganawar tasu ta mayar da hankali kan muhimamnci ci gaba da zaman lafiya da hadin kai a tsakanin dukkanin al'ummar kasar Masar kamar yadda aka sansua tarihinsu.
Hak nan kuma bayan kammala ganawar tawagar kiristocin ta mika kyautar kwafin kur'ani mai tsarki ga gwamnan na Minya.