IQNA

23:57 - September 09, 2018
Lambar Labari: 3482969
Bangaren kasa da kasa, kimanin yahudawan sahyuniya 150 ne suka kutsa kai cikin masallacin Quds mai alfarma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, mai magana da yuwun cibiyar kula da masallacin Quds Farras Dibs ya bayyana cewa, kimanin yahudawan sahyuniya 150 ne suka kutsa kai cikin masallacin Quds a yau.

Ya ce ministan harkokin noma na gwamnatin yahudawan Isra’ila Uri Aryal ne ya jagoranci yahudawan wajen cikin masallacin mai alfarma da nufin tsokanar Falastinawa.

Haka nan kuma ya ce yahudawan sun shiga cikin masallacin ne tare da cikakkiyar kariya daga jami’an tsaron Isra’ila, ta yadda Falastinawa ba za su iya hana su shiga cikin masallacin ba.

Jami’an tsaron Ira’ila sun yi awon gaba da daya daga cikin jami’an da suke kula da kwamitin masallacin Quds, sakamakon nuna bacin ransa kan keta alfarmar wannan wuri mai tsari da yahudawan suka yi.

3745265

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: