IQNA

Amurka Ta rufe Ofishin PLO Da Ke Cikin Kasarta

23:47 - September 10, 2018
Lambar Labari: 3482970
Babban sakataren kungiyar kwatar 'yencin Palasdinawa ta PLO Sa'ed Ariqat ya bayyana cewa matakin da Amurka ta dauka na rufe ofishin kungiyar a birnin Washington yana dai dai da azabtar da dukkan Palasdinawa ne.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ariqat yana fadar haka ne a yau litinin ya kuma kara da cewa wannan matakin wani karin azabtarwa ne wanda gwamnatin shugaban Trump na Amurka ta dauka, bayan dakatar da kudaden tallafi ga kiwon lafiya ilmi da kuma a halin yanzu kuma ofishin kungiyar PLO a washington.

Babban sakataren ya kara da cewa duk matakan da gwamnatin Amurka zata dauka na takuruwa al-ummar Palasdinu, al-ummar ba zata mika kai ga bukatun Amurka da HKI na amincewa da saryar da hakkin Palasdinawa ba.

Ya ce al-ummar Palasdinu ba ta sayarwa ba ce, don haka suna nan kan bakinsu na neman hakkinsu ta hanyoyin siyasa da dokokin kasa da kasa. 

Daga karshen sakataren yayi kira ga kasashen duniya su dauki mataki don kare al-ummar Palasdinu daga zaluncin gwamnatin Amurka da HKI.

3745492

 

 

captcha