IQNA

23:58 - September 11, 2018
Lambar Labari: 3482975
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar China tana yin liken asiri a kan ‘yan kasar mabiya addinin musulunci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin ‘yan kwanakin a ci gaba da takura ma musulmi da tae yi, gwamnatin kasar China tana yin liken asiri a kan ‘yan kasar mabiya addinin musulunci ta hanyoyi daban-daban.

Daga cikin hanyoyin da gwamnatin ta China ta bullo da su a halin yanzu, har da sauraren maganganu ta hanyar wayar salula da muuslmi suke yi, da kuma bibiyar shafukansu na yanar gizo.

Kafin wannan lokacin da gwamnatin ta China tana daykar matakan hana musulmi yin ayyuka na ibada, kamar azumi a cikin watan Ramadan, ko kuma hana su gudanar da wasu taruka na addini.

A halin yanzu dai kunhiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa suna sukar gwamnatin China kan hakan, tare da yin kira da ta sauya salon siyasarta  akan musulmin kasar marassa rinjaye.

3746140

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، china ، musulmi ، leken asisi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: