IQNA

23:34 - September 12, 2018
Lambar Labari: 3482976
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain ya fito a bainar jama'a tun fiye da shekaru biyu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya Talata babban malamin addinin muslunci na kasar Bahrain ya halarci taron farkon watan muharram a birnin London na kasar Birtaniya.

Wannan dais hi ne karo na farko tun fiye da shekaru biyu da masarautar kama karya ta kasar Bahrain ta hana alamin fita daga cikin gidansa, duk kuwa da matsananciyar rashin lafiyar da yake fama da ita.

Sakamakon matsin lamabr kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya, gwamnatin Bahrain ta kai malamin birnin London inda aka yi masa aikin tiyata, kuma har yanzu yake karbar magani.

3746316

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: