Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin DMCA ya bayar da rahoton cewa, dakarun sojion kasar Aljeriya sun fara kaddamar da wani farmaki a cikin tsaunukan Buwairah da ke tazarar kilomita 120 daga a gabashin birnin Algiers, da nufin cafke ko halaka jagoran alqaeda ayankin Magrib Abdulmalik Durkidal.
An haifi Durkidal a kasar Aljeriya ne a cikin shekara ta 1971, ya kuma halarci kasar Afghanistan inda ya yi yaki tare da kungiyoyin wahabiyawa masu tsatsauran ra'ayi.
A cikin shekara ta 2004 ya dawo Aljeriya ya zama jagoran kungiyar Salafiyya mmai tsatsauran ra'ayi a kasar, a cikin shekara ta 2006 ya zama jagoran kungiyar alqaeda a yankin.
Ana sa ran a wanna karon farmakin da aka fara kaddamarwa da nufin kame shi zai bayar da damar halaka shi ko kua kamshe tare da daruruwan 'yan ta'adda da suke tare da shi.