IQNA

Malamin Kur’ani Da Ya Bayar Da Rabin Albashinsa Ga Majami’a

23:59 - September 23, 2018
Lambar Labari: 3483007
Bangaren kasa da kasa, wani malamin kur’ani ya raba albashinsa biyu ya bayar da rabi ga wata majami’a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alkhalij online cewa, Usama Muhamma Najib wani malamin kur’ani ya raba albashinsa biyu ya bayar da rabi ga wata majami’a a lardin Minya.

Ya ce ya yi hakan ne bisa koyarwar kur’ani mai tsarki, inda  akowane lokaci kur’ani yana koyar da muuslmi yin aiki na kyautatawa ga wasu, muuslmi ne ko ba musulmi ba.

Bisa la’akari da muhimmancin taimakon juna tsakanin dukkanin mabiya addinai, wannan ya sanya shi yanke shawar yin wannan aiki ko da sau daya ne, domin muhimmancin da yake tattare da shi da kuma tasirinsa na isar da kakkyawan sako na sako na addinin musulunci.

3749075

 

 

 

 

 

 

captcha