IQNA

Jagora: Duk Masu Hannu A Harin Ahwaz Za Su Fuskanci Hukunci

22:55 - September 24, 2018
Lambar Labari: 3483008
Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya kara jaddada cewa, wadanda suke da hannu wajen kai harin ta'addanci a garin Ahwaz za su funkanci hukuncin da ya dace da su.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jagoran ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da 'yan wasan kasar Iran da suka samu lambobi a wasannin motsa jiki na kasashen Asia, wanda aka gudanar a kasar Indonesia.

Jagoran ya ce wadanda suka aikata wannan aikin ta'addanci a kan mata da kanan yara da kuma jami'ai masu kare kasa sun tabbata matsorata, domin gwaraza su ne matasan da suke aiki tukuru a fagagen ilimi da tsaron kasa da kuma wasani, kamar yadda matasan Iran suka tabbatar da hakan a lokuta daban-daban, daga ciki har da wasannin motsa jiki na nahiyar Asia.

A ranar assabar din da ta gabata ce wasu gungun 'yan ta'adda na kungiyar ta'addancin Al-ahwaziya dake samun goyon bayan mahukuntar biranan Riyad da Landon suka bude wuta kan jami'an tsaron Iran da fararen hula da suke gudanar da bikin makon tsaron kasa a garin Ahwaz da ke shiyar kudu maso yammacin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar mutane 29 da kuma raunana wasu 57 na daban.

Jim kadan bayan kai harin, Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei, ya mika sakon ta'aziyarsa ga iyalan shahidan da lamarin ya rusa dasu, sannan ya tabbatar da cewa wannan yauni ne da rataya a wuyan ma'aikatar leken asirin kasar data yi aikinta cikin tsanaki ta tantance ta kuma binciko suwa keda hannu a wannan harin domin gurfanar dasu gaban kotu.

Jagoran juyin juya halin Musulinci na Iran, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya ce wadannan 'yan ta'adda marasa imani da tausayi dake samun taimakon makiya masu da'awar karya , sun bude wa wadanda basu ji basu gani ba da suka hada da mata da yara wuta,saboda basa iya jurewa ganin karfin da Iran take da shi a cikin faretin sojojinta.

Mahimaiyar tambaya da za ta biyo bayan kai harin na Ahwaz shi ne su wanene suka kai wannan hari? shakka babu wadanda suka aiwatar da wannan ta'addanci 'ya'yan kungiyar nan ne na Ahwaziya dake samun goyon bayan Amurka da wasu kasashen yankin dake goyon bayan 'yan ta'addar takfiriya, a shekarar da ta gabata 'ya'yan wannan kungiya sun kai harin ta'addanci kan wata tawagar Iraniyawa dake ziyara a wuraren da aka yi yaki a shekarun baya, jamohoriyar musulinci ta Iran ta yi alawadai da kuma nuna rashin amincewarta da yadda aka bayar da dama ga kakakin wannan kungiyar ta 'yan ta'adda fitar da sanarwar daukan alhakin kai harin a wata Talabiji na birnin Landon.

Amurka da Saudiya gami da haramtacciyar kasar Isra'ila sun kirkiro kungiyoyin 'yan ta'adda a yanki da kuma daukan nauyinsu ne domin aiwatar da tsarinsu ne na ganin sun rusa kasashen musulinci.

Kamar yadda jagoran juyin juya halin musulinci ya bayyana wannan ta'addanci na a matsayin ci gaba da makircin kasashe 'yan amshin shatan Amurka a yanki, kuma manufarsu shine haifar da fitina da tashin hankali a wannan kasa, a don haka kasar Iran a koda yaushe zata ci gaba da dakile duk wani makircinsu.

Shakka babu, juriya da tsayin daka gami da 'yancin tsarin jamhoriyar musulinci na Iran, na daga cikin dalilan da ya sanya kasar Amurka ke nuna kiyayyarta karara kan al'ummar Iran,Harin ta'addancin na ranar assabar na zuwa ne bayan mumunan kashi da 'yan ta'adda suka sha a wasu kasashen.

3749792

 

captcha