IQNA

Saudiyya Tana Tsare Da Manyan Malamai 60

23:44 - September 24, 2018
Lambar Labari: 3483009
Rahotanni sun tabbatar da cewa a halin yanzu sannanun malaman wahabiya imanin 60 da masarautar Saudiyya take tsare da su, mafi yawa daga cikinsu ana tuhumarsu da laifin kin jinin salon siyasar Muhammad Bin Salamn ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, tun daga watan Satumban shekarar da ta gabata ta 2017 ya zuwa wannan watan Satmban da muke ciki, adadin mutanen da aka kame bisa dalilai na banbancin fahimta ko siyasa da makamantan haka, ya kai mutane 2613, daga cikinsu akwai malaman addini kimanin 60, sai kuma malaman jami'a 50, masu rajin kare hakkokin bil adama 20, lauyoyi 10.

A cikin shekarar da ta gabata ce Muhammad Bin Salman da sunan yaki da cin hanci da rashawa, ya kama wasu fitattun 'ya'yan gidan sarautar kasar da yake ganin za su iya zame masa barazana ga hankoronsa na darewa kan kujerar.

3749533

 

captcha