IQNA

Musulmin Amurka Sun Nuna Alhini Kan Harin Da Aka Kai A Majami’a

23:53 - October 28, 2018
Lambar Labari: 3483078
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Amurka sun nuna alhininsu dangane da kai harin da aka yi kan majami’ar yahudawa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai na Global News cewa, Scott Simpson shugaban wata kungiyar kare hakkokin musulmi a Amurka, ya bayyna cewa; musulmin kasar ta Amurka sun nuna alhininsu dangane da kai harin da aka yi kan majami’ar yahudawa a garin Petersbur.

Haka nan kuma ta hanyar cibiyarsa sun aike da sakonni da dama da nufin aikewa da su zuwa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, domin taya su alhihin abin da ya faru na kisan danginsu da wani mahari ya yi.

Scott Simpson ya ce cibiyarsa tana yin Allawadai da wannan danyen aiki a kan wurin ibadar yahudawa, kamar yadda take yin Allawadai dakai hari kan masallatai da cibiyoyin musulmi.

Babban alkalin alakalai n akasar Amurka ya ce ‘yan sanda sun kama wanda ya kai harin, baya ga haka kuma akwai wasu tuhumce-tuhumce guda 29 a kansa, saboda haka mai yiwuwa ya fuskanci hukuncin kisa.

3759473

 

 

 

captcha