IQNA

Jami’an Tsaro Sun bayar Da Kariya Ga Masu Taron Arbaeen A India

23:54 - October 29, 2018
Lambar Labari: 3483080
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar India sun bayar da kariya ga masu gudanar da tarukan arbaeen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin News Indiana cewa, a yau ne musulmi mabiya mazhabar shi’a mazauna birnin Petne da ma wasu yankuna na kasar india suka gudanar da tarukan arbaeen.

Bayanin ya ce jami’an tsaron sun dauki tsauraran matakai domin bayar da kariya ga masu gudanar da wadannan taruka, musamman a yankunan Darvazeh da kuma Manara Bazar, inda aka aike da ‘yan sanda masu yawan gaske.

A kowace shekara dai a cikin daruruwan shekaru da suka gabata, mabiya mazhabar shi’a  akasar India suna gudanar da irin wannan taro, duk kuwa da cewa a halin yanzu lamarin ya hada har da wasu daga cikin muuslmi da suke shiga ana gudanar da taron tare da su.

An kammala dukkanin tarukan da aka gudanar a yau na arbaeen a kasar India ba tare da samun wata hatsaniya ba, sakamakon ayyukan hadin gwiwa da ake yi tsakanin masu tarukan da kuma jami’an tsaro, domin tabbatar da cewa komai ya tafi lafiya kamar yadda aka tsara.

3759748

 

 

 

captcha