IQNA

Musulmi Sun Taimaka Ma yahudawan Da Aka Kaiwa Hari A Amurka

23:48 - October 30, 2018
Lambar Labari: 3483086
Bangaren kasa da kasa, wasu kungiyoyin musulmin Amurka biyu sun tara tallafin kudade domin taimakawa Yahudawan da aka kai musu harin ta'addanci a garin Pittsburgh da ke jihar Pennsylvania ta kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna  ya watsa rahoton cewa: Wasu kungiyoyin musulmi biyu sun bude gidauniyar tattara taimakon kudade domin tallafawa Yahudawan da aka kaddamar da harin wuce gona da iri kansu a garin Pittsburgh da ke jihar Pennsylvania ta kasar Amurka.

Har ila yau kungiyoyin musulmin biyu sun jaddada aniyarsu ta gudanar da aiki tare da kungiyoyin Yahudawan Amurka da nufin wanzar da zaman lafiya da sulhu a tsakanin al'ummar kasar, kuma a halin yanzu kudaden da suka tattara zasu fara amfani da su wajen gudanar da jiya ga Yahudawan da suka samu raunuka gami da bisine wadanda suka rasa rayukansu a yayin kaddamar da harin kansu.

A ranar Asabar da ta gabata ce wani mutum mai suna Robert Bowers dan shekaru 46 a duniya ya bude wuta kan mai uwa da wabi kan taron jama'a da mafi yawansu Yahudawa ne a garin Pittsburgh na kasar Amurka, inda ya kashe mutane sha hudu  tare da jikkata wasu sha biyu na daban. 

3759713

 

 

 

captcha