IQNA

Falastinawa 316 Ne Suka Yi Shahada A Cikin Wannan Shekara

23:55 - November 01, 2018
Lambar Labari: 3483090
Bangaren kasa da kasa, tun daga lokacin da Trump ya shelanta birnin Qods a matsayin babban birnin Isra’ila ya zuwa yanzu Falastinawa 316 ne suka yi shahada.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daga lokacin da Trump ya dauke ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Qods a matsayin babban birnin Isra’ila ya zuwa yanzu Falastinawa 316 ne suka yi shahada, daga ciki har har da kananan yara 68 da kuma ‘yan gwagwarmaya 19.

Bayanin y ace kimanin 204 daga cikin wadanda suka yi shahada daga yankin zirin Gaza suke, yayin da saurtan kuma daga yankunan Quds da gabar yamma da kogin Jordan da sauransu.

A ranar 6 ga watan Disamban 2016 ne dai shugaban Amurka ya shelata dauke ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel aviv zuwa Qods, lamarin da ya fuskanci adawa daga kasashen duniya, kuma tun daga lokacin Falastinawa suna ci gaba da bijirewa wannan kudiri.

3760428

 

 

 

 

 

captcha