IQNA

Taro Mai Taken Manzon 'Yan Adamtaka A Iskandariyya

22:42 - November 08, 2018
Lambar Labari: 3483113
Bangaren kasa da kasam an gudanar da wani taro mai taken manzon 'yan adamtaka a yankin Iskandariyya na kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da zaman taro mai taken manzon 'yan adamtaka a lardin Iskandariyya na kasar masar tare da halartar malamai da kuma dalibai, bisa umanin Muhammad Mukhtar Juma'a ministan harkokin addini na kasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa, a wurin taron malamai sun gabatar da jawabai kan matsayin manzon Allah a bangaren rayuwa ta zamantakewa a cikin al'umma, ta yadda halayensa suke a matsayin babban darasi da za a koyi da su.

Halayen manzon  Allah (saw) halaye ne masu dacewa da kowane irin yanayi na al'ummomi, da hakan ya hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, domin kuwa halayensa suna koyar da hakikanin kyawawan dabi'u ne na dan adam.

Wanna taro dai yana zuwa nea  lokain da ake gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin wafatinsa, kuma ake shirin shiga watan rabiul awwal mai alfarma, wanda aka haife shi a ciki.

3762287

 

 

 

 

captcha