IQNA

Iran Ta Raba Kwafin Kur'anai Da Liffai A Uganda

22:47 - November 14, 2018
Lambar Labari: 3483125
Bangaren kasa da kasa, an raba kwafin kur'anai da kuma littafan addini a kasar Uganda a lokacin gudanar da tarukan Maulidi.

Kamfanin dillancin lbaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, an raba kwafin kur'anai da kuma littafan addini a kasar Uganda a lokacin gudanar da tarukan Maulidin manzon Allah.

Tarukan dai ana gudanar da su ne a birane daban-daban da musulmi suke musamman ma a birnin kapala fadar mulkin kasar, inda musulmi da dama suke rayuwa a cikinsa.

Baya ga kwafin ur'anai akwai littafai na addini da suka shafi na tarihin muslunci da kuma na sanin hukunce-hukunce da sauransu, domin raba wag a makarantun addini.

Kasar Uganda na daga cikin kasashen gabashin Afrika da suke da kyakkyaawar alaka da kasar Iran.

3763861

 

 

 

 

 

captcha