Kamfanin dillancin labaran Anadol ya bayar da rahoton cewa, Farncisca Giffy minister mai kula da harkokin iyalaia kasar Jamus ta bayyana cewa, bisa la'akari da yadda kyamar addinai ke karuwa a cikin makarantun kasar, hakan ya sanya ala tilas ma'aikatarta ta dauki matakin da ya dace.
Ta ce wannan lamari ne da yake bukatar aiki na hadin gwiwa a tsakanin ma'aikatarta da sauran ma'aikatu, musamman ma ma'ikatr ilimi ta kasar.
Kasar Jamus na daga cikin kasashen da musulmi suka fi yawa a tsakanin kasashen nahiyar turai, amma a cikin shekarun baya-bayan nan musulmi suna fuskantar matsaloli na tsangwama, musamman a yankunan da ma su tsatsauran ra'ayin kiyayya da baki suke.