IQNA

Jami'an Tsaro Sun Halaka Mai Ba Wa Daesh Fatawa A Iraki

21:31 - December 07, 2018
Lambar Labari: 3483194
Jami'an tsaron gwamnatin Iraki sun samu nasarar halaka babban jigo kuma mai bayar da fatawa ga 'yan ta'addan Daesh a Iraki.

Shafin yada labarai na Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, Anad Sa'adu babban kwamandan rundunar sojin Iraki a lardin salahuddin ya bayyana cewa, a yau Juma'a dakarunsa tare da hadin gwiwa da sojoji sa kai na hashd Shabi, sun kaddamar da wani farmaki a kan duwatsun Hamarain da ke arewa masu gabashin birnin Tikrit.

Ya ce an kaddamar da farmaki na yau ne bayan samun wasu bayanai na sirri kan wuraren da 'yan ta'addan Daesh suke boyea  cikin dwatsun na hamrain, daga cikinsu har da babban mai basu fatawa Hamis Jisam Al-Falu, wand aka samu nasarar halaka shia  farmakin na yau Juma'a.

A cikin shekara ta 2014 ce Al-Falu ya bayar da fatawar kasha dukkanin maza a cikin kabilar Al-jaburia  cikin lardin salahuddin, tare da aura matansu baki daya ga 'yan ta'adda.

3770277

 

captcha