IQNA

Mutane Miliyan 70 Ne Ba Su Iya Rubutu Da Karatu A Najeriya Ba

8:13 - December 11, 2018
Lambar Labari: 3483205
Bangaren kasa da kasa, shugaban hukumar yaki da jahilci a Najeriya Abba Haladu ya bayyana cewa, kimanin mutane miliyan 70 ne suke fama da matsalar jahilci a Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Abba Haladu shugaban hukumar yaki da jahilci a Najeriya ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, a halin yanzu kimanin mutane miliyan 70 ne suke fama da matsalar rashin iya rubutu da karatu a Najeriya baki daya.

Y ace wannan adadi yana da yawa matuka idan aka kwatanta da yawan al’ummar kasar, inda hakan ke nuni da cewa adadin mutanen ya kai kashi 35 cikin dari daga cikin mutane miliyan 200 da suke rayuwa a Najeriya.

Ya kara da cewa, bisa binciken da aka gudanar yara kimanin miliyan 11 ne ba su makaranta a halin yanzu a Najeriya, yayinn da adadin masu fama da matsalar rashin ita karatu da rubutu kusan miliyan 60 daga cikin matasa ne da kuma masu yawan shekaru.

Ya ce akwai abubuwa da dama da suka jawo haka, daga cikin akwai matsaloli tsakanin al’umma na rashin jituwa saboda dalilai na addini ko kabilanci, sai kuma babbar matsalar da tafi ciwa kasar tuwo a kwarya ta rashin gudanar da lamurra yadda ya kamata, da kuma cin hanci da rashawa da yayi katutu a cikin harkokin gudanarwa a kasar.

3771104

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha