IQNA

Jagora: Za A Gudanar Da Tarukan Cika Shekaru 40 Na Nasarar Juyin Musulunci

23:19 - December 12, 2018
1
Lambar Labari: 3483208
Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Ayatollah Khamenei ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka tana taimakawa gwamnatin kasar saudia a ta'asar da take aikatawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Jagoran ya bayyana haka ne a lokacinda yake ganawa da iyalan shahidai a gidansa a yau laraba, ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana taimakawa kasar Saudia a yakin da ta fara a kasar yemen tun shekara ta dubu biyu da sha biyar, yakin da take tsammanin zata kammalashi a cikin yan makonni ko watanni idan yayi yawa. 

A wani wuri a jawabinsa jagoran ya ce gwamnatin kasar Saudia tana hada kai da makiya addinin musulunci wajen cutar da musulmi.

Dangane da takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar Iran kuma jagoran ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran tana kara karfi duk tare da matsin lamban da Amurka takewa kasar, kuma Amurka bata yi wani abu a bayaba kuma nan gaba ma da yardar Allah ba zata iya yin kome ba. 

Jagoran ya yi watsi da fatan da gwamnatin Amurka take yi na cewa gwamnatin Jamhuriyar musulunci ta Iran ba zata ga bakin cika shekaru 40 da samuwar Jamhuriyar musulunci ta Iran ba. wato a shekara ta dubu biyu da sha tara.

Daga karshe jagoran ya bayyana sunan da Imam Khomanini  wanda ya kafa Jamhuriyar musulunci ta Iran ya bawa Amurka na cewa ita ce babbar Shaitan, ya farkar da mutanen duniya hakikanin yadda gwamnatin Amurka take.

Jagoran ya jadda cewa ko shakka babu a wannan karon al’ummar kasar Iran za su kara baiwa maras da kunya, domin kuwa za su fito a ranar cika shekaru arbain da samun nasara juyin mulsunci fiye da kowane lokaci.

Abin tuni a na dais hi ne, Amurka da ‘yan korenta na yankin gabas ta tsakiya sun sha alwashin cewa an gama gudanar da tarukan murnan tunawa da zagayowar juyin musulunci a Iran, inda suke cewa a wannan karon za a yi taron kawo karshen juyin ne, wanda hakan ne ma babban dalilin fiwar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya, bayan karbar cin hanci na daruruwan biliyoyin daloli daga wata kasar larabawa, da nufin a haifawarwa Iran matsalar tattalin arziki, ta yadda mutane za su yi bore domin hakan ya kawo karshen juyin musulunci a kasar.

 

3771828

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Mustafa Manyankasa
0
0
Yakamata kasar saudiyya su fahimci abinda yahadasu da iran yafi abinda yarabasu wato musulunci adaina nufin juna da sharri
captcha