IQNA

Musulmi Da Kirista Suna Kamfen Yaki Da Wariya A Canada

23:24 - December 12, 2018
Lambar Labari: 3483210
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci da kuma mabiya addinin kirista a kasar Canada suna gudanar da kamfe na hadin gwiwa  a tsakaninsu domin yaki da nuna wariya ta addini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, shafin yada labarai na London Free Press ya bayar da rahoton cewa, a jiya mabiya addinin muslunci da kuma mabiya addinin kirista a garin London na jahar Ontario a kasar Canada suna gudanar da kamfe na hadin gwiwa  a tsakaninsu domin yaki da nuna wariya ta addini a fadin kasar.

Wannan kamfe dai da nufin ganin an kawo karshen nuna duk wani abun da ya shafi banbanci ga jama'a saboda addininsu ko akidarsu, domin kuwa hakan shi ne babban abin da yake haifar da kiyayya da kyamar juna a tsakanin mutane.

Haka nan kuma kamfen din na da nufin karfafa zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban da suke zaunea  kasar ta Canada tare da gudanar da komai nasu a cikin zaman lafiya da fahimtar juna.

A cikin 'yan lokutan baya-bayan nan an samu bullar mutane masu tsananin kiyayya ga musulmi a kasar Canada, duk kuwa da irin matakan da hukumomin kasar suke dauka na dakile irin wannan nuna kyama, wanda hakan ya sake kunno kai ne a kasar sakamakon sabuwar siyasar Amurka a yanzu, wadda ke nuna kiyayya da kyama ga wani bangare na al'umma.

3771790

 

 

captcha