IQNA

Darul Fatawa A Masar Ta Halasta Taya Kiristoci Murnar Bukukuwansu

23:01 - December 14, 2018
Lambar Labari: 3483217
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta bayar da bayani kan halascin taya kiristoci murnar zagayowar lokutan bukuwan sabuwar shekarsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Alahram ya bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta bayar da bayani kan halascin taya kiristoci murnar zagayowar lokutan bukuwan sabuwar shekarsu da suke gudanarwa a kowace shekara.

Bayanin ya ce babu wani wuri da aka hana yin hakan, saboda haka matukar ba a samu hani ba, to babu laifi a kan yin haka, musamman idan aka yi la'akari da cewa hakan yana da babban tasiri wajen kara kusanto da mabiya addinain biyu wuri daya tare da samar da zaman lafiya.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, a halin da duniya take a yanzu, musulmi suna da bukar yin amfani da hanyoyi na hkima a cikin dukkanin lamurra da suka shafi zamantakeawarsu da auran al'ummomi da mabiya addinai daban-daban.

Baya ga hakan kuma bayanin y ace wannan zai kara fito da kyakyawarr fuskar musulunci wadda ta ginua  kan girmama dan adam da mutunta ra'ayinsa da mahangarsa, da kuma zaman lafiya tare da sauran mabiya addinai.

3772252

 

 

captcha