IQNA

Jagora Ya Jagoranci An Gudanar Da Jana'izar Ayatollah Hashemi Shahrudi

23:46 - December 26, 2018
Lambar Labari: 3483253
An gudanar da janazar babban malamin addinin muslunci Ayatollah Shahrudi a yau, wanda Allah ya yi masa rasuwa a jiya .

Kamfanin labaran iqna, Jagoran huyin juya halin muslucnia  Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ne ya jagoranci janazar wadda aka gudanar a birnin Qom tare da halardar dubban daruruwan jama'a.

An bizne gawarsa a cikin hubbaren Sayyida Faima Ma'asuma jikar manzon Allah (SAW) da ke birnin Qom, inda kuma ake bizne gawawwakin manyan malamai da suka gabata a birnin tun daruruwan shekaru da suka gabata.

Mafi yawa daga cikin manyan jami'an gwanatin kasar Iran da manyan malamai sun halarci janazar, kamar yadda kuma akwai baki daga kasashen duniya daban-daban da suka halarci janazara a yau.

A daren yau kuma ana zaman karbar gaisuwar ta'aziyarsa a birnin na Qom, tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei da sauran manyan malamai.

3775756

 

 

 

 

captcha