IQNA

Rauhani Ya Aike Da Sakonni Taya Murna Sabuwar Shekara Ga Shugabannin Kasashe

23:54 - January 01, 2019
Lambar Labari: 3483272
Shugaban kasar Iran Hassan Rauhani ya aike da sakonni an taya mayrnar shiga sabuwar shekara miliyadiyya ta 2019 ga shugabaniin kasashen duniya daban-daban.

A cikin sakon nasa, shugaba Rauhani ya fatan wanann sabuwar shekara ta Miladiyya za ta zama shekara mai alhairi ga dukkanin al'ummomi na duniya, tare da samun samun kwanciyar hankali da zaman lafiya ci gaba.

Haka nan kuam ya kirayi sauran takwarorinsa na kasashen duniya, da su hada hannu wuri guda domin yin aiki tare a bangarori daban-daban domin ciyar da kasashensu gaba, domin al'ummominsu su samu kyakkyawar rayuwa.

Daga karshe Rauhai ya jaddada muhimmancin kara hada karfi da karfe tsakanin dukkanin manyan jagorori na addinai a duniya, domin samun fahimta  atsakanin mabiyansu, domin samun zaman lafiya da sulhu a tsakanin al'ummomi na duniya.

 

3777309

 

 

captcha