IQNA

Wani Babban Jami’i Libya Ya Fita Daga Kungiyar Ikhwan

16:13 - January 27, 2019
Lambar Labari: 3483333
Bangaren kasa da kasa, Khalid Almushri shugaban majalisar shugabancin kasar Libya ya fita daga kungiyar Ikhwan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya Khalid Almushri shugaban majalisar shugabancin kasar Libya ya sanar da fita daga kungiyar Ikhwan muslimin.

Ya ce bisa la’akari da nauyin da ke kansa na al’umma, ya zama wajibi ya dauki irin wannan mataki, domin ya zama ya yi adalci a cikin aikinsa, saboda haka ya fita daga kungiyar Ikwan a matsayinsa na mamban kungiyar.

Haka nan kuma Khalid Ya bayyana cewa, duk da ya fice daga kungiyar, amma zai ci gaba da gudanar da sauran hidimominsa kamar yadda ya saba na siyasa da na jama’a domin ci gaban al’ummar kasaLibya.

Tun bayan faduwar gwamnatin Mu’ammar Ghaddafi ne dai kungiyar Ikhwan ta samu wurin zama  acikin harkokin sisyasar kasar Libya, inda mambobin kungiya ne suk tafiyar da majalisar mulkin kasar.

3784794

 

 

 

captcha