Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na freemalaysiatoday cewa, an samar da wani sabon mashin ATM a kasar Malysia wanda za a rika yin amafani da shi domin bayar da taimakon abinci.
Bayanin ya ce za a fara amfani da wannan sabon mashin a baban masallacin Kualalmpour fadar mulkin kasar Malaysia daga nan zuwa karshen wannan wata.
Kakin masallacin ya bayyana cewa, babbarmanufar samar da wannan hanya ita ce bayar da taimako cikin sauki ga mabukata.
Tun kafin wannan lokaci dai an jima ana tattauana yadda za a bullo da wannan shiri, wanda zai yanzu aka samu damar aiwatar da shi.