Kamfanin dillancin labaran iqna, a yau musulmi a kasar India a birane daban-daban sun yi zanga-zangar nuna adawa da ziyarar Muhammad birnin Salman da aka shirya zai kai yau a kasarsu.
Wannan zanga-zanga an gudanar da irinta akasar Pakistan a ranar 17 ga wannan wata Fabrairu da akshirya cewa yariman Saudiyya zai kai ziyara a kasar, wanda hakan yasa ala tilas aka dage ziyarar zuwa ranar 18 ga wata.
An dai shirya cewa ayau Bin Salman zai nufi kasar India, amma a can ma dai zanga-zangar ta fara gabatar zuwan nasa, inda wanda kuma musulmi ne suke gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ziyarar tasa.
Babban abin da yasa Bin Salman ke fusntar zanga-zanga duk inda ya nufa a halin yanzu a duniya shi ne kisan Jamal Khashoggi, da kuma hannun da yake da shi a kisan al’ummar kasar Yemen.