IQNA

Hukuncin Dauri A Bahrain A Kan Mutane 170 Bisa Goyon Baya Ga Ayatollah Qasem

23:57 - March 01, 2019
Lambar Labari: 3483416
Bangaren kasa da kasa, masarautar mulkin kama karya a kasar Bahrain tanadaure ‘yan kasar da suka nuna goyonbaya ga babban malamin addini na kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yanar gizo na Almanar ya bayar da rahoton cewa,  masarautar mulkin kama karya a kasar Bahrain ta yanke hukuncin daurin shekaru a gidan kaso a kan ‘yan kasar da suka nuna goyonbaya ga babban malamin addini na kasar Ayatollah Sheikh Isa Qasem.

Rahoton ya ce masarautar mulkin kama karya ta Bahrain ta yanke hukuncin daurin shekaru tsakanin daya zuwa goma a kan mutane 170 da ta ce an same da laifin nuna goyon baya ga babban malamin addinin kasar ayatollah Isa Kasim.

Yanzu haka dai shehin malamin baya cikin kasar ta Bahrain tun bayan da ya fita zuwa kasashen waje domin neman magani, kafin lokacin dai masarautar ta janye hakkinsa na zama dan kasa, kamar yadda kuma ta hana shi yin mu'amala da mutane, tare da jige daruruwan 'yan sandaa kofar gidansa.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun yi Allawadai da wannan hukunci wanda yake na siyasa ne, da kuma muzgunawa duk wani mai ra'ayi na siyasa da ya sabawa na mahukuntan kasar.

3794006

 

captcha