IQNA

Gwamnatin China Na Tilasta Mata Musulmi Auren Maza Wadanda Ba Musulmi Ba

18:50 - March 12, 2019
Lambar Labari: 3483451
Gwamnatin kasar China taa ci gaba da kara daukar matakai na kara takura musulmi a kasar.

tashar Ala'arabiyya ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar China ta fara daukar wasu matakai a halin yanzu na tilasta 'yan mata musulmi auren maza wadanda ba musulmi ba a kasar.

Wannan mataki yana zuwa bayan daukar wasu matakan na gallaawa musulmi, da hakan ya hada da hana gudanar da ayyukan ibada kamar azumi da makamantan hakan a lokacin watan ramadan, kamar yadda kuam ake tilasta su cin namana alade ko hana su yin salla a kan lokaci.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama a duniya sun gargadi gwamnatin kasar China kan wannan lamari, inda wasu daga cikin kungiyoyin suka shirya rahotanni tare da gabatar da sua  gaban kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya.

3797196

 

 

 

captcha