IQNA

Babu Yanayi Na Cutar Da Musulmi A Jamus Inji Gwamnatin Kasar

23:08 - March 20, 2019
Lambar Labari: 3483476
Gwamnatin kasar Jamus ta ce yanayin kasar ba zai bayar da damar a cutar da musulmi a kasar ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus Horst Seehofer, a lokacin da yake zantawa da jaridar Beld ta kasar Jamus a ranar Litinin da ta gabata ya bayyana cewa, kasarsa tana yanayi mai kyau a dukaknin bangarori na zamantakewa, zaman lafiya tsaro da kuma doka da oda.

Ya ce bisa irin wannan yanayi da kasar jamus take da shi, babu wata dama da za a iya cutar da musulmia  cikin kasar, ya ce duk kuwa da cewa akwai wasu 'yan tsiraru masu tsatsauran ra'ayi, amma ba su karfin halin da za su iya auka wa musulmi domin cutar da su.

Haka nan kuma ministan ya nuna takaicinsa dangane da abin da ya faru na harin New Zealand, inda wani dan ta'adda ya kashe musulmi hamsina  cikin masallaci, inda ya ce gwamnatin Jamus ba za ta taba bari wani ya kai hari kan masallatai ko cibiyoyin musulmi ba, kuma ana daukar matakai na basu kariya yadda ya kamata.

 

3798959

 

captcha