IQNA

Zarif Ya Soki Siyasar Amurka A Kan Kasashen Musulmi

23:27 - March 23, 2019
1
Lambar Labari: 3483483
Ministan harkokin wajen Iran, Muhammad Jawad Zarif ya wallafawannan batun ne a shafinsa na Twitter sannan ya kara da cewa; Amurka ce ummul haba’isin duk wani rashin zaman lafiya a cikin yankin gabas ta tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Zarif ya kara da cewa; Rudar kai ne wata kasa ta zaci cewa tana kara karfi ta hanyar karya dokokin kasa da kasa, da nuna wa kasashe masu cin gashin kansu karfi, ko kuma tatsar wasu kasashe.

Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma kara da cewa; Abubuwan da suke faruwa suna nuni ne da karatowar lokacin durkushewar daula.

Sakon na ministan harkokin wajen Jamhuriyar musulunci ta Iran, yana a matsayin Mayar da martani ne ga wani sako da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya wallafa da a ciki yake yin kira da Amurka ta yarda da cewa; Yankin tuddan Gulan na Syria mallakin haramtacciyar kasar Isra’ila ne.

Kungiyoyin kasa da kasa da su ka hada tarayyar Turai sun yi tir da kalaman na shugaban kasar Amurka tare da bayyana shi a matsayin wanda yake cin karo da dokokin kasa da kasa.

3799420

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
allah ya shiga tsakaninmu damakiya muslinci
captcha