Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, a ranar Asabar shugaban mabiya addinin kirista ‘yan darikar Katolika Paparoma Francis zai ziyarci kasar Morocco
Kimanin mutane 30,000 ne mabiya adinin kirista za su taru domin i tarbarsa, akasarinsu dai ‘yan kasashen Afrika ne da suke karatua kasar ta Morocco.
Haka nan kuma zai jagoranci wani taron addinin a babban filin wasanni na birnin Rabat, tare da halartar mabiya addinin kiista kimanin dubu 10.
Wannan dais hi ne karo farko da wani jagoran kiristoci na duniya zai ziyarco Morocco tun daga shekara ta 1985, a lokacin paparoma John Pol ya ziyarci kasar.
Sarki Hassan na biyu shi ne wani shugaban larabawa da ya gayyaci paparoma zuwa kasarsa, kuma a shekara ta 1991 shi ma ya ziyarci fadar Vatican.