IQNA

Paparoma Francis Na Ziyara A Morocco

23:47 - March 31, 2019
Lambar Labari: 3483507
Shugaban darikar katolika na duniya, Paparoma Francis, na wata ziyara a kasar Morocco, mai manufar tattaunawa ta tsakanin addinai da batutwuan ci gaba da kuma matsalar bakin haure.

Paparoma na wannan ziyarar ce bisa goron gayyatar sarki Mohammed VI, na kasar ta Morocco, mai kunshe da musulmi kasha 99%.

An tsara a yayin ziyarar sarkin na Morocco da Paparoma Francis, zasu gudanar da jawabigaban dandazon jama’a, wanda kuam za’a watsa a manyan akwatinan talabijin.

An kuma tsara jagoran darikar ‘yan katolikan zai ziyarci cibiyar bayar da horo ga limamai ta kasa da kasa ta birnin Rabah, wanda kuam shi ne karo na farko da wani Paparoma ya ziyarci wannan cibiyar.

Ko a watan Fabrairu da ya gabata ma, Paparoman ya gudanar da irin wannan ziyarar a kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Masar, inda duka dai ziyarar ta maida hankali kan fahimtar juna da kuma zaman tare da kuma baiwa kowa damar gudanar da addininsa.

3800396

 

 

captcha