IQNA

Fira Ministan Iraki na Zimmar Kusanto Da Mahanga Tsakanin Tehran Da Riyad

22:27 - April 06, 2019
Lambar Labari: 3483523
Bangaren kasa da kasa, Pira ministan na kasar Iraki Adel Abdul Mahadi ya iso birnin Tehran dazu da safe, domin fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Wanann shi ne karo na farko da Pira ministan na Iraqi ya kawo ziyara Iran bisa gayyatar da shugaban kasa Dr. Hassan Rauhani ya yi masa.

A karkashin tawagar Pira ministan na Iraki da akwai manyan jami’an gwamnati da na tattalin arziki, domin tattaunawa da takwarorinsu na Iran da su ka hada da mininstan harkokin waje Muhammad Jawad Zarif.

Bugu da kari tawagar ta Iraki za ta halarci wani zaman hadin guiwa a karkashin cibiyar tattalin arziki ta kasashen biyu.

A gobe Lahadi idan Allah ya kaimu, Pira ministan na kasar Iraki zai ziyarci hubbaren Imam Ridha (AS) dake birnin Mashhad a yankin arewa maso yammacin kasar.

A cikin watan Maris, shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya kai ziyarar kwanaki biyar a kasar Iraki.

3801254       

 

 

 

 

 

 

 

captcha