Kamfanin dillancin labaran iqna, Ministan tsaron kasar Laftanar Janar Awad ne ya sanar da hakan a wani jawabi da yayi inda ya sanar da kawo karshen gwamnatin al-Bashir din ta tsawon shekaru talatin da kuma tsare shi a wani waje da bai bayyana ko ina ba ne.
Har ila yau kuma sanarwar sojin ta sanar da kafa dokar ta baci na tsawon watanni uku a kasar, kamar yadda kuma sojojin za su ci gaba da kula da kasar da kuma shirye-shiryen mika mulki cikin shekaru biyu, haka nan kuma sun sanar da dakatar da kundin tsarin mulkin kasar.
Kifar da gwamnatin Bashir din ta zo ne sakamakon zanga-zangar da al’ummar kasar suka dinga yi tsawon watanni da bukatar ya sauka daga karagar mulki.
To sai dai kungiyoyin da suka jagoranci zanga-zangar musamman kungiyar Sudanese Professionals Association sun yi watsi da sanarwar soji da cewa babu wani abin da ya sauya, don haka suka kirayi masu zanga-zangar da su ci gaba da zanga-zangogin na su har sai an biya musu bukatunsu.