IQNA

23:50 - April 17, 2019
Lambar Labari: 3483554
Rahotanni daga Sudan na cewa an kai hambararen shugaban kasar Umar Hassan Al-Bashir a wani gidan kurkuku dake Khartoum babban birnin kasar.

Kmafanin dillancin labaran iqna, Bayanai da kamfanin dilancin labaran Reuters ya samu daga wasu majiyoyi a gidan yarin, sun tabbatar da cewa an kai tsaohon shugaban kasar ta Sudan a gidan yarin, inda ake tsare da shi cikin kwararen matakai na tsaro.

Dama kafin hakan kamfanin dilancin labaren faransa ya nakalto daga wata majiya daga iyalen hambararen shugaban cewa, an wuce da shi a gidan yarin Koberdake birnin Khartoum.

Tun da farko dai mahukuntan rikon kwarya na sojin kasar, sun shaida cewa ana tsare da hambararren shugaban kasar a cikin wani wuri mai aminci.

A Ranar 11 ga watan Afrilun nan ne sojoji su ka kifar da mulkin shugaba Umar Hassan Al’Bashir, , sakamakon bore na kin jinin gwamnatinsa daga jama’a kasar, wanda ya samo asali bayan wani matakin gwamnati na kara kudin biredi, wanda daga bisani kuma ya rikide zuwa na kyamar mulkinsa , bayan shafe shekaru talatin yana mulkin kasar.

3804676

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Albashir ، sudan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: