Kamfanin dilalncin labaran iqna, za a gudanar da tarukan nisf shaaban a birnin berlin na kasar Jamus kamar yadda a aka saba a kowace shekara.
Majiyoyin cibiyar ahlul bait da ke birnin Berlin sun ce a yau an fara gudanar da dukkanin shiryeshiren da suka kamata domin gudanar da taron ranar sha biyar ga watan Sha'aban.
Daga cikin abubuwan da aka yi a yau har da raba abinci da abin sha ga mutane masu wucewa a gaban cibiyar musulmi da wadanda ba muuslmi ba, domin murnar zagayowar wannan rana mai albarka.
A gobe idan Allah ya kai mu za a gudanar da jawabai dangane da matsayin ranar, da jawabai kan Imam mahdi amincin Allah ya tabata a gare shi.