Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na tashar Almanar ya bayar da rahoton cewa, a yau kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi tir da Allawadai da munanan hare-haren da aka kai a otel-otel da kuma majami’un mabiya addinin kirista a kasar Sri Lanka.
Bayanin ya kungiyar Hizbullah ya bayyana harin da cewa aiki ne na ta’addanci, wanda yake kara tabbatar da cewa ta’addanci ba shi da addini, domin kuwa kai hari a wurin ibada na mabiya wani addini aiki ne na dabbanci da rashin imani.
Kungiyar Hizbullah tya nisanta abin da ya faru da addinin muslunci, tare da bayyana shi da cewa aiki ne na mutanen da ba su san wani addini ba, balantana kimarsa , ko kuma kimamar mabiyansa, kamar yadda kuma ‘yan ta’adda ba su girmama hatta addinin da suke ikirarin cewa suna biyayya gare shi da dokokinsa.
Hare-Haren ta’addancin da aka kai kasar ta Sri Lanka dai sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 207, tare da jikkata wasu fiye da 450, wadanda wasu daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali.