IQNA

Musulmi Dubu 200 Ne Suka Halarci Babban Taron Musulmin Faransa

21:42 - April 22, 2019
Lambar Labari: 3483568
Ana gudanar da babban taron shekara-shekara na musulmin kasar Faransa tare da halartar mutane kimanin dubu 200.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoto day a nakalto daga kafofin yada labaran Faransa daga birnin Paris cewa, tun kwanaki uku da suka gabata ne aka fara gudanar da babban taron mabiya addinin musuluci na kasar Faransa, wanda yake gudana a kowace shekara.

Wannan dai shi ne karo 36 da ake gudanar da wannan taro wanda shi ne taron musulmi mafi girma  anahiyar turai baki daya., tare da halartar musulmi kimanin dubu 200 daga sassa na kasar ta Faransa.

Haka nan kuma a wanann karon an gayyaci wasu sauran mabiya addinai daga sassa  na kasar ta Faransa dmin halartar taron, inda ake yin bayanai dangane da addinin musulunci da kuma koyarwarsa, tare da gabatar da makaloli, da kuma baje kolin kayayyaki da suke nuni da al’adu na tarihin musulunci.

Babbar manufar taron dai ita ce kara fito da matsayin addinin muslucni a kan lamurra da dama da suke shige wa wasu duhu, musamman ma wadanda ba musulmi, domin su san abin da musulunci yake koyarwa na daga kyawawan halaye da kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin dukkanin bil adama.

3805451

 

captcha