IQNA

Jagora: Dole Ne A Karfafa Alaka Ta Tsakanin Iran da Pakistan

21:20 - April 23, 2019
Lambar Labari: 3483571
Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa yan ta’adda sun so su dagula dangantaka mai kyau da take tsakanin kasashen Iran da Pakistan.

Jagoran ya bayyana haka ne a jiya Litinin a lokacinda yake ganawa da Fraiministan kasar Pakistan Imran Khan wanda yake ziyarar aiki a kasar. Jagoran ya kara da cewa makiya kasashen biyu ne suke tallafawa yan ta’adda wadanda suke kai hare-hare a kan iyakokin kasashen biyu, sannan ya bukaci kasashen biyu su hada kai don ganin an karfafa dangantakar dake tsakaninsu duk tare da matsalolin da ake samu nan da can.

Dangane da dadedden tarihin danganta tsakanin kasashen biyu kuma, jagoran ya ce kasashen yankin Asia ta kudu sun sami ci gaba sosai ne a lokacinda musulmi suke iko da yankin.

A nashi bangaren Fraiministan kasar Pakistan Imran Khan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Pakistan a wannan ziyarar ta tattauna da bangaren Iran kan matsaloli da dama, kuma tuni sun cimma yerjeniyoyi a kansu.

Imran Khan ya kara da cewa gwamnatin Pakistan zata ci gaba da tuntubar gwamnatin Iran don ganin babu wata matsala da zata shiga tsakanin kasashen biyu.

Kafin haka dai Fraiministan ya gana da shugaban kasa Dr Hassan Ruhuna, sannan sun gabatar da jawabi hadin guiwa ga yan jaridu dangane da abubuwan da suka tattauna a kansu.

3805676

 

captcha