IQNA

Taron karatun Kur’ani Mai Tsarki A kasar Burkina Faso

21:32 - April 23, 2019
Lambar Labari: 3483574
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman karatun kur’ani mai tsarki a babban masallacin ‘yan darikar Tijjaniya a kasar Burkiya Faso.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da zaman karatun kur’ani mai tsarki a babban masallacin ‘yan darikar Tijjaniya da ke fadar mulkin kasar Burkiya Faso, wanda wata cibiyar ‘yan shi’a karkashin jagorancin Tijjani samawi daga Tunisia ta dauki nauyin shiryawa.

Wannan taro dai na zuwa a daidai lokacin da ake gudanar ad taruka na watan sha’aban, domin shirin shiga watan Ramadan mai alfarma.

Kasar Burkina Faso dai tana daga cikin kasashen yammacin Afrika, kuma mafi yawan musulmin kasar mabiya darikar Tijjaniya ne.

3805736

Taron karatun Kur’ani Mai Tsarki A kasar Burkina Faso

Taron karatun Kur’ani Mai Tsarki A kasar Burkina Faso

Taron karatun Kur’ani Mai Tsarki A kasar Burkina Faso

captcha