IQNA

An Zargi Paparoma Da kawo Bidi’oi A Cikin Addinin Kirista

23:58 - May 02, 2019
Lambar Labari: 3483599
Wasu kirista sun zargi Paparoma da kawo wasu sabbin bi’oi da ba a san su a  cikin addinin kirista ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Euronews ta bayar da rahoton cewa, wasu manyan  malaman addinin kirista da kuma wasu masana kiristoci, sun rubuta wata wasika zuwa bababn malamin addinin kirista na darikar Katolika Paparoma Francis, inda suke zarginsa da saka wasu sabbin bidi’oi a cikin addinin na kirista.

Wanann wasika ta kunshi shafuka 20 tare da sanya hannun manyan malaman addinin kirista daga kasashe daban-daban na turai, inda suke tunatar da paparoma kana bin da yafi dacewa domin kiyaye koyarwar addinin nasu.

Sai a nasa bangaren kakain fadar Vatican wanda kan yi magana da suna Paparima bai ce uffan a kan wanann batu ba.

Daga cikin wadanda suka rattaba hannu kan wannan wasika da aka aikewa Paparoma, har da fitaccen malamin addinin kirista na kasar Birtaniya Aiden Nicolas da shkaru 70, wanda ya rubuta littafai masu tarin yawa a kan akidar addinin kiristanci.

3808152

 

 

 

 

 

captcha