IQNA

Dan Majalisar Iraki: Kaiwa Iran Hari Zai Rusa Martabar Amurka A Duniya

22:28 - May 09, 2019
1
Lambar Labari: 3483622
Dan majalisar dokokin kasar Iraki ya bayyana duk wani yunkuri da Amurka za ta wajen kaiwa kasar Iran harin soji da cewa, hakan zai sanya ta rasa matsayinta a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna,a  zantawar da ya yi da tashar Al-alam Hassan Salim dan majalisar dokokin kasar Iraki ya bayyana cewa, idan Amurka ta yi gigin kaiwa kasar Iran harin soji, to kuwa lallai za ta ji kunya, domin kuwa daga lokacin za ta rasa abubuwa da dama da take takama sua  gabas ta tsakiya.

Ya kara da cewa, babbar wadda abin zai fi shafa ita ce babbar ‘yar lelan Amurka wato Isra’ila, inda hakan zai iya zama masomin rushewarta baki daya.

Haka nan kuma dan majalisar dokokin kasar ta Iraki ya bayyana kada kugen yakin da Amurka take yi a  kan Iran da cewa; duk da cewa wasu daga cikin kasashen larabawa da na musulmi sun riga sun zama ‘yan amshin shata ga Amurka, amma hakan ba ya nufin cewa musulmi da dama a aduniya ba su tare da Iran.

3810174

 

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Musa mohammed yusuf
0
0
Wannan gaskiyane. Allah yakara ruguza kafurci da kafirai.
captcha