Kamfanin dillancin labaran iqna, an bude bangaren kasa da kasa a wannan bababn baje kolin kur'ani na kasa da kasa da ke samun halartar bangarori daban-daban daga cikin gida da kuma kasashen duniya.
Mamhud Wa'izi wanda shi ne babban jami'i mai kula da bangaren kasa da kasa, a wannan baje koli ya bayyana cewa, daga abubuwan da aka baje a wanann bangaren akwai littafai na Urdu, Ingilishi, Larabci, da Turkanci, da kuma mujallar Tunisia.
Pakistan ita ce babbar bakuwar bangaren, haka nan kuma kasashen ad suke halarta sun hada da Iraki, malaysia, Yemen, Afghanistan Tunisia da sauransu.