Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Alamnar ta bayar da rahoton cewa, ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar Masar ta sanar da cewa, jami’an tsaro sun kai farmakia wata maboyar ‘yan ta’adda a cikin yankin Jiza, kuma sun samu nasarar kashe 12 daga cikinsu.
Bayanin ya ce an kai wanann samam ne bayan samun bayanan sirri dangane da kai komon mutanen da ake zargin cewa suna da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda, bayan tabbatar da lamarin, an kai farmaki tare da halaka su.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani harin ta’addanci da aka kai masu wasu masu yawan bude ne a garin na Jiza, inda aka kashe mutane 14 daga cikinsu, daga ciki kuwa har da ‘yan kasar Afrika ta gudu su biyu.
Kasar Masar dai ta fara fama da matsalolin tsaro ne tun bayan juyin mulkin da Abdulfattah Sisi ya yi tsohon shugaban kasar ta Masar.